Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya

[ad_1]



Al’ummomin ƙananan hukumomin da ke yankin Arewacin Jihar Neja sun gudanar taron Sallah da addu’o’i na musamman domin neman Allah Ya kawo musu zaman lafiya, sakamakon matsalar ’yan bindiga da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Hare-haren ’yan bindiga ya yi ajalin dubban mutane tare da raba su da muhallnasu da hanyoyin samun arziki a sassan Jihar Neja da wasu sassan Najeriya.

Ga hotunan;

Dubban jama’a daga yankin ƙananan hukumomi shida da ke Arewacin Jihar Neja sun gudanar da addu’a ta musamman domin samun tsaro da aminci.
Manta da ƙananan yara sun fito Filin Idi na Kontagora domin halartar taron addu’o’in da aka gudanar a ranar Asabar.
Mutane daga ƙananan hukumomin Magama, Borgu, Rijau Mashegu da Kontagora na daga cikin yankunan da hare-haren ’yan bindiga suka fi addaba a Jihar Neja.
’Yan ta’adda sun kashe mutane sun sace wasu da dama tare da dabbobi, baya ga ƙona gidaje da dukiyoyi, tare da tilasta wa dangin waɗanda aka sace biyan kuɗaɗen fansa.
An sace dubban mutane, yawancinsu mata da magidanta a sassan Jihar Neja wadda ke fama da matsalar ’yan bindiga kamar maƙwabtansa jihohin Kwara, Kaduna, Kebbi, Zamfara da Katsina da Kogi da da Babban Birnin Tarayya


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *