AFCON 2025: Super Eagles Sun Murƙushe Mozambique Da Ci 4–0
[ad_1]
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta nuna bajinta a gasar Kofin Kasashen Afrika (AFCON) 2025 bayan ta doke ƙasar Mozambique da Ƙwallaye 4–0 a wasan zagayen ba 16 da aka buga.
Wasan, wanda ya fara da misalin karfe 8:00 na dare agogon Nijeriya, ya ƙayatar matuƙa, musamman ga magoya baya dake kallon Super Eagles a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƴan takarar lashe kofin a wannan karo. Nijeriya ta mallaki wasan tun daga farko, tana matsa lamba kan abokiyar karawarta.
- Za A Biya Super Eagles Kyautar Miliyan 14.5 Kan Kowace Ƙwallon Da Suka Ci A Wasa Da Mozambique
- An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
Ademola Lookman ne ya fara buɗe kofa da zura ƙwallo bayan kyakkyawan taimako daga Akor Adams ta gefen hagu. Kafin a tafi hutun rabin lokaci, Victor Osimhen ya ƙara wa Nijeriya ƙwallo ta biyu, lamarin da ya sa aka tafi 2–0 a mintuna 45 na farko.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Osimhen ya sake zura ƙwallo ta biyu a wasan, wacce ta zama ta uku a gare shi a gasar bana. Daga bisani Akor Adams ya kammala cin ƙwallaye da ta hudu, inda ya tabbatar da cikakken rinjaye.
Nijeriya yanzu za ta jira zuwa ranar Talata domin sanin ƙasar da za ta kara da ita a wasan kusa da na ƙarshe (Quarter Final).
[ad_2]
Source link