Tinubu zai yanke shawara kan tura sakamakon zaɓe ta intanet – Hadiminsa
[ad_1]
Mai bai Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yanke hukunci kan batun tura sakamakon zaɓe ta intanet, bisa la’akari da halin da ƙasar ke ciki a yanzu.
Aminiya ta rawaito cewa Majalisar Dattawa ta amince da dokar gyaran tsarin zaɓe, wadda ta ƙaddamar da tura sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓe zuwa shafin INEC (IReV) ta intanet, sai dai an tanadi cewa za a iya amfani da tsarin takarda idan aka samu matsalar sadarwa ko rashin intanet.
Wannan matakin ya biyo bayan kwanaki na zanga-zangar kungiyoyin fararen hula da suka nemi Majalisar ta tabbatar da tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet daga rumfunan zaɓe.
A wata hira da gidan talabijin na ARISE, Sunday ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa shugaban ƙasa zai yi abin da ya dace da ƙasar.
“Ina tabbatar muku cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda kowa ya san ɗan dimokuraɗiyya ne, zai yi abin da ya dace, amma ba zai yi hakan ba tare da la’akari da halin da ƙasar ke ciki ba,” in ji Sunday.
Ya kuma yi tambaya kan yiwuwar cikakken tura sakamakon kai tsaye, yana mai cewa babu wata ƙasa da ke da tsarin intanet da ba ya samun matsala.
“Babu inda ake samun kashi 100 cikin 100 na tura sakamakon kai tsaye. Shin kuna nufin cewa wannan ƙasa ta riga ta samu tana da cikakken sabis din intanet din da zai ba ta damar yin hakan gaba ɗaya?” ya tambaya.
A gefe guda, jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa shugaban ƙasa yana jin tsoron tura sakamakon zaɓe kai tsaye ne saboda yana tsoron faduwa zabe.
A cewar PDP, duk da cewa a baya Tinubu ya sha kiran a rika yin zabe na zamani, amma kuma yanzu da yake da damar aiwatar da hakan yana tsoron yi saboda fargabar faduwa zabe.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link