An Yi Nasarar Gwajin Rokar Dakon Kaya Ta “Changzheng” Da Kumbon “Mengzhou” Mai Dauke Da ‘Yan Sama Jannati

[ad_1]

Hukumar kula da ayyukan kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati ta kasar Sin (CMSA) ta ba da labari cewa, a yau Laraba a cibiyar harbar rokoki ta Wenchang dake kudancin kasar Sin, an cimma nasarar aikin gwaji na rokar dakon kaya na “Changzheng” mai lamba 10 da ake fi sani da “Long March-10”, da kumbon dake dauke da ‘yan sama jannati na “Mengzhou”, inda aka tantance karfin rokar a wurin dake kusa da doron kasa, a bangaren karfin sarrafawa da ba da jagorancin zirga-zirga da sadarwa da sauran abubuwa masu alaka, da kuma aikin gwajin tseren gudu na kumbon “Mengzhou” mai dauke da ‘yan sama jannati, wanda ke da ma’ana wajen ba da tabbaci ga ‘yan sama jannati wajen fita daga rokar ba tare da jin rauni ba, lokacin da suka gamu da hadari a sararin samaniya.

Wadannan su ne jerin ayyukan gwaji da Sin take gudanarwa yayin da take kokarin nazari da kirkiro kumbo da roka domin zirga-zirga a samarin samaniya, tun bayan gwajin kunna wuta na rokar “Long March-10” da gwajin tsere a yanayi maras nauyi da gwajin tashi da saukar kumbuna na “Lanyue” da ake fatan ya sauka a duniyar wata. Matakin da ya bayyana cewa aikin binciken duniyar wata na Sin mai amfani da ‘yan sama jannati ya samu wani muhimmin ci gaba a matakin.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *