An Samu Gagarumin Ci Gaba Wajen Kafa Kasuwar Lantarki A Sin

[ad_1]

Bisa labarin da aka samu daga hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin, bayan shekaru da dama, nau’in samar da wutar lantarki na Sin ya sauya daga tsarinsa na farko zuwa tsarin da ake amfani da shi a kasuwa, inda ya samu babban ci gaba wajen kafa hadaddiyar kasuwar wutar lantarki ta kasa.

An gabatar da cewa, kafin karshen shekarar 2025, yawan cinikin tsarin wutar lantarki da ke kasuwa a Sin ya kai awar kilowatt tiriliyan 6.6, kusan ya ninka sau bakwai bisa na 2015, kuma kason da ke cikin jimillar amfani da wutar lantarki ya tashi daga kasa da kashi 15% zuwa 64%. Ban da wutar lantarki mai kare ginshikin samar da lantarki wanda ake samarwa don amfanar da wannan tsari, duk sauran nau’o’in wutar lantarkin ana yin cinikinsu ne ta kasuwa.

Bugu da kari, ana sadar da wutar lantarki cikin ’yanci a yawancin sassan kasar, tare da samun karuwar ma’aunin cinikin wutar lantarki tsakanin larduna da yankuna, daga kasa da awar kilowatt tiriliyan 0.1 a 2015 zuwa kimanin awar kilowatt tiriliyan 1.6 a 2025.(Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *