Rashin Isassun Makarantu Ke Sa Ana Yi Wa Yara Auren Wuri A Arewacin Nijeriya – Sarkin Kano

[ad_1]

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce ana yi wa yara auren wuri a wasu sassan Arewacin Nijeriya ne saboda gwamnati ba ta samar da isassun makarantu da damammaki ga ‘yan mata bayan kammala firamare ba.

Da yake magana a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels, Sanusi ya bayyana cewa yawanci yara mata makarantar firamare kaɗai suke gamawa.

  • Zaɓen 2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jama’a Kan Kalaman Ƙiyayya Da Labaran Ƙarya A Kano
  • ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane, Sun Ƙone Gidaje A Ƙauyukan Kwara

‘Yan mata na kammala makaranta tun suna kusan shekara 11, amma babu makarantar sakandare, cibiyoyin koyon sana’a ko wasu hanyoyin ci gaba da ilimi.

Ya ce hakan na sa iyaye marasa ƙarfi su shiga fargaba game da abin da zai faru da ‘ya’yansu mata tsakanin shekaru 11 zuwa 18.

Saboda tsoron lalacewa ko fadawa cikin matsala, da yawa daga cikinsu sukan yanke shawarar aurar da ‘ya’yansu da wuri.

Duk da cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa kowane yaro na da haƙƙin samun ilimi, Sanusi ya ce ba a aiwatar da wannan doka yadda ya kamata, domin gwamnati kanta ba ta gina isassun makarantu ba, musamman a karkara.

Sarkin ya jaddada cewa ba za a iya magance auren yara ta hanyar zargin al’ada kaɗai ba.

A cewarsa, dole ne gwamnati ta zuba jari a fannin ilimi da walwalar jama’a domin bai wa ‘yan mata damammaki.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *