Dambarwar Da Ta Biyo Bayan Sauya Sheƙar Gwamna Yusuf Na Jihar Kano


Batun sauya sheƙa daga wata jam’iyyar siyasa zuwa wata, wani alamari ne da yake da dogon tarihi a siyasar Nijeriya, tun daga jamhuriyar siyasa ta farko kamun akai ga samun ‘yancin-kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya.

Manyan ‘yan siyasa irin su marigayi Malam Aminu Kano da Malam Sa’adu Zungur da ire-irensu, jam’iyyar NPC suka fara yi farko, kafin su tattara kayansu zuwa jam’iyyar NEPU. A wannan zamani kuma, irin su jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi sauye-sauye a tsakanin Jam’iyyun PDP, APC, da NNPP a yanzu.

  • Muhimmanci Da Amfanin Shan Rake Ga Lafiyar Dan Adam
  • Hotuna: Babbar Mota Ta Hallaka Wata Bafulatana A Bauchi

Rikicin da ya dabaibaye batun sauya sheƙar gwamna Yusuf na jihar Kano daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC, inda wasu ke ganin hakan butulci ne ga maigidansa Kwankwaso wasu kuma ke ganin hakan ba laifi ba ne, lissafin siyasa ne kawai.

A cewar masu ganin laifin gwamna Abba, suna nanata cewa, “tun da Kwankwaso ne silar Abba ya zama gwamnan Kano, lallai ne ya ci gaba da zama tare da shi a siyasance, da daɗi da ba daɗi.”

In ba a manta ba, A ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, Gwamnan Jihar Kano ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC, bayan ya sanar da yin murabus daga NNPP a ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026, ƙasa da shekaru uku bayan lashe zaben gwamnan Kano.

Gwamnan ya ce rikicin cikin gida, rikicin shugabanci da shari’o’i a kotu, sun raunana jam’iyyar tare da raba kan mambobinta.

Ya ƙara da cewa, komawarsa APC za ta ba shi damar yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da Gwamnatin Tarayya domin kawo ayyukan raya ƙasa da ci gaban Kano.

Wannan na ɗauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya hannu a ranar Juma’a.

Ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon tunani, inda ya ce zai ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Kano.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa mambobi 21 na Majalisar Dokokin Jihar Kano, mambobi takwas na Majalisar Wakilai, da shugabannin ƙananan hukumomi 44 sun fice daga NNPP tare da gwamnan.

Duk da cewa, Gwamna Abba ya nannata cewa, ya yi shawarwari da na gabanshi a siyasa kafin sauya sheƙar amma abun mamaki sai ga maigidansa a siyasa, Jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yana cewa, duk wanda ya yi masa butulci sai ya yi nadama.

“Ficewar Gwamna Abba daga NNPP ta zo wa mutane da yawa mamaki, ya ƙara da cewa shi ma da farko ya ji kamar mafarki ne,” in ji Kwankwaso.

Don haka, Kwankwaso ya bayyana ranar 23 Ga Janairu a matsayin Ranar Cin Amana ta Duniya.

Itama a nata ɓangaren, jam’iyyar NNPP cewa ta yi, sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir zuwa jam’iyyar APC cin amana ne ga jam’iyyar, jagoranta Sanata Rabiu Kwankwaso, da kuma al’ummar Kano.

Kakakin NNPP, Ladipo Johnson, ya ce jam’iyyar ba ta da ƙarfi sosai a Kano kafin zaɓen 2023, amma ta samu nasara ne saboda tasirin Kwankwaso da goyon bayan jama’a.

Jim kaɗan bayan sauya sheƙar gwamnan a hukumance wanda aka yi bikin murna a babban ɗakin taro na ‘Coronation Hall’ da ke gidan gwamnatin Kano, a yayin da yake jawabi, ɗaya daga cikin manyan baƙi, tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya shaidawa gwamnan cewa, babu wanda zai yi takara da shi a zaɓen 2027 mai zuwa, inda shi ma, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya umurci duk mabiyan sa da su yi wa gwamna Abba mubaya’a.

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Abdulsalam Gwarzo, bai halarci taron sauya shekar maigidansa, gwamna Yusuf ba zuwa jam’iyyar APC, wanda hakan ke nuna gagarumin saɓani a siyasar jihar kafin babban zaɓen 2027.

Bayan haka, an samu rahotonnin wasu Kwamishinoni da masu riƙe da muƙaman siyasa duk sun yi murabus daga muƙamansu don nuna ɓacin ransu da kuma jaddada mubaya’arsu ga jagoran tafiyar aƙidar Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *