Za A Gudanar Da Dandalin Tattaunawa Na Masana Na Jam’iyyar JKS Da KMT A Birnin Beijing
[ad_1]
Kakakin ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin Zhang Han, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a jiya Laraba cewa, sakamakon cimma daidaito tsakanin jam’iyyar kwaminis ta Sin wato JKS, da jam’iyyar Kuomintang wato KMT, za a gudanar da dandalin tattaunawa na masana na jam’iyyun biyu a ranar 3 ga watan Fabarairu a birnin Beijing, inda wakilai da masana daga jam’iyyun biyu, da bangarorin masu yawon shakatawa, da masana’antu, da jami’an kiwon lafiya, da na kiyaye muhalli da sauransu, za su yi mu’amala, da tattaunawa kan batutuwan dake shafar gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan a fannonin yawon shakatawa, da sana’o’i, da kiyaye muhalli, da hadin gwiwa mai dorewa da sauransu, ta yadda za a tattauna lalubo hanyoyin raya huldar dake tsakanin gabobin biyu, da kuma amfanar da jama’arsu baki daya. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link