Kashi 11 ne kawai na makarantun Najeriya ke da ruwa da banɗaki — UNICEF
Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya ce Najeriya na fuskantar babbar barazana ga lafiyar jama’a da harkar ilimi, sakamakon kashi 11 cikin 100 ne kawai na makarantu a faɗin ƙasar da ke da ruwa da banɗaki mai tsafta.
Babban jami’in UNICEF, Rahamah Farrah ne, ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da kafafen yaɗa labarai da aka gudanar a Kano a ranar Laraba.
Ya ce rashin samun tsaftataccen ruwa da banɗaki a makarantu da cibiyoyin lafiya na janyo ɗalibai, musamman ’yan mata rashin zuwa makaranta, tare da jefa miliyoyin yara cikin hatsarin kamuwa da cututtuka irin su kwalara da zazzabin cizon sauro.
“Makarantu da cibiyoyin lafiya su ne ginshiƙin lafiyar yara da iliminsu. Idan babu tsaftataccen ruwa da banɗaki, yawan rashin zuwa makaranta na ƙaruwa.
“Cututtuka masu yaɗuwa kuma na saurin bazuwa, wanda ke kawo cikas ga ƙoƙarin Najeriya na cimma manufofin ci gaba mai ɗorewa,” in ji Farrah.
Ya bayyana cewa duk da cewa jihohin Jigawa da Katsina sun samu ci gaba wajen rage yin bahaya a waje, jihohi da dama a Arewa maso Yamma har yanzu an bar su a baya.
Ya ƙara da cewa kayan wanke hannu da sauran kayayyakin tsafta a waɗannan jihohi ba su taka kara sun karya ba.
A cewarsa, UNICEF tare da tallafin Gwamnatin Birtaniya, ta zuba fam miliyan 19 a cikin shirin gina kayayyakin more rayuwa masu jure sauyin yanayi na CRIPS, inda aka samar da cibiyoyin lafiya da ilimi 84 a Kano da Jigawa a bara.
Ya ƙara da cewa yanzu ana faɗaɗa shirin zuwa jihohin Bauchi, Gombe, Kaduna da Katsina.
Farrah, ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da su ƙara taka rawa wajen ɗora wa gwamnati alhaki kan yadda ake ware kasafi da aiwatar da kayayyakin tsafta.
“Labaranku na iya ƙara asassa muryar yara da kuma matsa lamba ga masu yin doka da su bai wa shirin muhimmanci a kasafi,” in ji shi.
Da ta ke wakiltar Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Kano (SUBEB), Sakatariyar hukumar, Hajiya Amina Umar, ta ce jihar Kano na da makarantu 8,782, waɗanda suka haɗa da firamare 7,331 da kuma ƙananan sakandare 1,451.
Ta ce daga cikin waɗannan makarantu, 5,884 ne ke da kayayyakin tsaftace jiki a halin yanzu.
“Muna son tabbatar da cewa dukkanin makarantu sun samu ruwan sha, kuma muna aiki tare da abokan hulɗarmu domin cimma hakan.
“Wannan tattaunawa za ta ƙara mana ƙwarin gwiwa wajen ƙara himma. SUBEB ta riga ta haɗa ɓangaren wannan shiri cikin ayyukanta.”
A nasa ɓangaren, Daraktan Muhalli da Lafiyar Jama’a na Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko na Kano, Sani Abdullahi Ungogo, ya bayyana cewa jihar na da cibiyoyin lafiya a matakin farko 1,239, amma 282 ne kawai ke da kayayyakin tsafta.
“Waɗannan cibiyoyi yanzu sun samu tsaftataccen ruwa, banɗaki, kwandon shara da sauran muhimman abubuwa. Muna aiki don faɗaɗa wannan zuwa sauran sassan jihar, kuma muna maraba da shawarwari da za su taimaka mana mu samu ci gaba,” in ji shi.
Ungogo ya ƙara da cewa hukumar na kula da ɗaruruwan asibitoci da cibiyoyin lafiya a faɗin Kano, kuma ta ƙudiri aniyar faɗaɗa ayyukanta domin kare lafiyar al’umma.