Binciken CGTN: Tsarin Diflomasiyyar Amurka Na Babakere Ya Tada Hankula Kan Jagorancin Duniya
[ad_1]
Manufar harkokin waje ta fifita “Amurka a kan komai” ta haifar da damuwa mai yawa a tsakanin al’ummomin duniya. A cewar wani bincike na jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a tsakanin masu amfani da shafukan intanet na duniya, kusan kashi 90.7 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi Allah wadai da Amurka saboda nuna son shugabancin kasa da kasa alhali kuma ta ki daukar nauyin da ya rataya a wuyanta a harkokin jagorancin duniya, inda suka kalli hakan a matsayin wani abu da ke nuna tsarin diflomasiyya na babakere baro-baro a fili.
A yayin da ake tsaka da caccakarta da yi mata zanga-zanga, Amurka ta janye daga Hukumar Lafiya ta Duniya da Yarjejeniyar Paris a hukumance. A cikin binciken jin ra’ayoyin, kashi 57.8 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa wannan matakin da Amurka ta dauka zai yi mummunan tasiri ga al’amuran duniya kamar na jagorancin sha’anin lafiyar jama’a da kuma kula da yanayi.
Bugu da kari, har yanzu Amurka tana dauke da bashin biyan hakki ga Hukumar Lafiya ta Duniya da ya kai dala miliyan 260, inda a game da hakan, kashi 81.9 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyi suka yi kira ga Amurka da ta biya kudin da ake bin ta cikin gaggawa. Daga shekarar nan ta 2026, Amurka ta janye daga hukumomi da kungiyoyi daban-daban na duniya, wadanda suka shafi fannoni da dama na jagorancin duniya, ciki har da na kula da yanayi, lafiyar jama’a, ilimi, al’adu, ’yan gudun hijira, da kuma samar da ci gaba mai dorewa.
Kazalika, a cikin binciken, kashi 83.4 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun caccaki Amurka saboda halin ko-in-kula da take nunawa game da jagorancin duniya, inda suka yi tir da hakan a matsayin “nuna karfin iko na banza”, yayin da kuma kashi 85.3 cikin dari suka yi imanin cewa manufar fifita “Amurka a kan komai” ta zubar da kimar kasar da bata mata suna a duniya.
Binciken jin ra’ayoyin jama’ar na CGTN wanda aka wallafa a cikin harsunan Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci da Rashanci, ya sami bayyana ra’ayoyi daga mutane 7,379 cikin sa’o’i 24. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link