Kudaden Bincike Da Samar Da Ci Gaba Na Kamfanonin Gwamnatin Sin Sun Ci Gaba Da Haura Yuan Tiriliyan Daya Cikin Shekaru Hudu A Jere
[ad_1]
A yau Laraba, mataimakin shugaban hukumar sanya ido da jagorancin kadarorin gwamnatin kasar Sin, karkashin majalisar gudanarwar kasar Pang Xiaogang, ya ce jimillar kudaden da kamfanoni mallakin gwamnatin tsakiya ta Sin ke kashewa a fannonin bincike da samar da ci gaba, sun ci gaba da haura kudin kasar yuan tiriliyan daya cikin shekaru hudu a jere.
Pang ya ce a shekarar 2025 da ta gabata, rukunin wadannan kamfanoni sun zuba jarin da ya kai yuan tiriliyan 1.1, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 157.69 a ayyukan bincike da samar da ci gaba.
Jami’in ya kara da cewa, ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, darajar jimillar kadarori mallakin gwamnatin tsakiyar kasar Sin sun haura yuan tiriliyan 95, kana sun samar da ribar da ta kai ta yuan tiriliyan 2.5, da darajar kadarori na zahiri da suka kai yuan tiriliyan 5.1.
Pang Xiaogang, ya ce hakan zai ingiza dunkule ci gaban kamfanonin dake tattaro ababen sarrafawa, da masu samar da hajoji da rarraba su cikin tsarin shigar da hajojin sassan duniya, kana hakan zai samar da karin tallafi ga cimma nasarar muhimman kudurori, da ayyukan raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da Sin ta sanya gaba. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link