Jam’iyyu 10 ne za su fafata a zaɓen cike gurbi a Kano — INEC




Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta sanar da cewa jam’iyyun siyasa guda 10 ne za su shiga zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano da za a gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Kwamishinan Zaɓe na Jihar Kano (REC), Ambasada Abdu Zango ne, ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kano.

Ya ce hukumar ta karɓi sunayen ’yan takara daga jam’iyyu 10 domin zaɓen da za a yi a ƙananan hukumomin Birni da Ungogo.

Jam’iyyun sun haɗa da APC, ADP, AAC, PRP, Dennis Labour Party, APGA, Good Party, Action Alliance, Labour Party da NNPP.

“Mun samu bayanan ’yan takara daga jam’iyyu 10. A halin yanzu ana ci gaba da ɗora bayanan ’yan takara a shafin INEC, kuma hedikwata ce za ta tabbatar da adadi na ƙarshe da aka samu,” in ji Zango.

Ya ce duk da cewa an miƙa sunayen a matakin jiha, jam’iyyu a matakin ƙasa ne ke da alhakin ɗora bayanan ’yan takara a shafin INEC na Intanet.

INEC ta kuma ce ta sanya ido kan yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwani na jam’iyyun kuma ba a samu rahoton wata matsala ba.

“Masu sa ido na INEC sun duba yadda jam’iyyu suka gudanar da zaɓukansu, kuma zuwa yanzu ba mu samu rahoton maguɗi ko kura-kurai ba,” a cewarsa.

Zango ya ƙara da cewa INEC ba ta samu wata sanarwa daga kotu ko umarni da ya shafi shugabancin kowace jam’iyya ko gudanar da zaɓukan fidda gwani ba, ciki har da NNPP.

Kwamishinan zaɓen ya tabbatar wa jama’a cewa shirye-shiryen gudanar da zaɓen yi nisa, kuma INEC ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Ya ce ƙananan hukumomin biyu suna da sama da mutane 535,000 da suka yi rajista da kuma da rumfunan zaɓe sama da 1,000.

INEC ta buƙaci dukkanin masu kaɗa ƙuri’a a yankunan da abin ya shafa da su fito ƙwansu da kwarkwata domin amfani da ’yancinsu, tare da tabbatar da cewa an tanadi isassun jami’ai, tsaro da kayayyaki domin gudanar da sahihin zaɓe.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *