Wuta ta kona wani mutum har lahira a Kwara
[ad_1]
Wutar daji ta kona wani matsahin malamin addinin Kirista har lahira a gidansa da ke yankin Irewolede a garin Ilori, hedikwatar Jihar Kwara.
Fasto Samson Awolola mai shekara 37 ya gamu da ajalinsa ne a ranar Litnin, bayan da ya kunna wuta domin kona ciyayi a wani kangonsa da yake gini.
Shaidu sun bayyana cewa wutar da yake kona ciyayin ce ta bazu cikin gaggawa, inda ta rista da shi ya kasa fita daga cikin filin wanda aka katange.
Sun bayyana cewa leburan da mamacin ya kawo domin yi masa aiki a filin ya tsallake rijiya da baya ta hanyar tsallake katangar.
Shi ma Fasto Awolola ya yi yunkurin tsallake katangar domin tsira da ransa, amma ya kasa, wutar ta tsare shi a ciki.
Daga baya jami’an kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar kafin ta bazu zuwa gidajen makwabta, amma duk da haka Fasto Awolola ya rasa ransa.
Ya bayyana cewa, “An ciro gawar Fasto Awolola aka mika ta ga shugaban al’ummar yankin, Mista Sunday Nuha, domin yin sauran abubuwan da suka kamata.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link