Yawan Kudaden Da Baki Suka Kashe A Sin Ya Karu A Shekarar Bara
[ad_1]
Kwanan baya, babbar hukumar kula da harkokin haraji ta kasar Sin, ta yi nazari kan yadda ake kashe kudi a cikin kasar Sin bisa bayanan da ta tattara game da karbar haraji. Nazarin ya nuna cewa, a shekarar 2025, an samu wasu sabbin ci gaba cikin kasuwannin kasar Sin, inda bukatun al’umma kan na’urorin lantarki da ake amfani da su a cikin gida, da wayoyin salula, da motocin lantarki sun karu inda kuma ake ci gaba da kirkire-kirkire kan sabon tsarin yin sayayya, da sabon yanayin yin sayayya.
A sa’i daya kuma, an samu karin kudin shiga bisa haduwar harkokin yawon bude ido da al’adu, sabon tsarin yin sayayya ya kuma bunkasa bisa ci gaban fasahohin zamani, kana, bukatun al’umma kan hidimar motsa jiki, da kiwon lafiya sun karu kamar yadda ake fatan gani, yayin da karuwar yawon tsoffi a kasar ta bunkasa sayayyar da ake yi a fannin hidima, da kayayyakin da ake samarwa tsoffi.
Ban da haka kuma, an cimma nasarar kyautata yanayin yin sayayya ga bakin da suke zuwa kasar Sin, wanda hakan ya sa yawon kudin da baki suka kashe a kasar Sin ya karu a shekarar 2025, kana yawan bakin da suka yi rajistar mayar da haraji a lokacin da suka koma gida ya karu da kaso 305 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2024.
Bugu da kari, jimillar kudaden da suka kashe kan hajojin da aka mayar musu haraji ya karu da kaso 95.9 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2024. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link