Ana zargin magidanci da yin lalata da agolarsa mai shekara 12 a Bayelsa
[ad_1]
An zargi wani magidanci mai shekaru 40 da yin lalata da wata ’yar da yake riko mai shekaru 12 a Obunagha, karamar hukumar Yenagoa ta jihar Bayelsa.
Makwabta a yankin sun ce yarinyar ta shiga cikin matsanancin hali, inda aka garzaya da ita Asibitin Jami’ar Yankin Neja Delta (NDUTH), Okolobiri, tana zubar da jini daga gabanta da sauran matsaloli.
Matasa ne dai suka cafke wanda ake zargin, wanda aka bayyana a matsayin mai aikin gini a unguwar, bayan sun ji kukan yarinyar tare da ganin jinin da ke fita daga jikinta.
Sun yi masa dukan tsiya kafin su mika shi ga rundunar Aiki ta ’yan sanda.
Uban yarinyar, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, inda ya tabbatar da cewa yarinyar tana karkashin kulawa ta musamman a asibiti.
Ya ce iyalan suna shirin neman a gurfanar da wanda ake zargi a kotu bayan tattaunawa.
Tsohon shugaban matasan Gbarain Youths Federation, Pere Orufa, ya tabbatar da lamarin, yana cewa wanda ake zargi ya taɓa aikata hakan a baya da sanin mahaifiyar yarinyar.
“Amma da ya sake yi, yarinyar ta shiga matsanancin ciwo kuma ta fara zubar da jini. Sai mahaifiyar ta yi ihu, hakan ya sa matasan suka cafke shi,” in ji shi.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya da mugunta, ya kuma shawarci mata su kasance masu lura, musamman waɗanda suka sake aure bayan rabuwa da mazajensu, domin kare ’ya’yansu daga cin zarafi.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar, DSP Musa Muhammad, ya ce lamarin yana hannun rundunar ta Aiki kuma ba a mika shi ga rundunar a jihar ba tukuna.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link