Salah ya koma atisaye a Liverpool

[ad_1]

Mohamed Salah ya koma atisaye a Liverpool wannan Talatar bayan kammala gasar Kofin Afirka (AFCON), yayin da ƙungiyar ke shirin fafatawa da Marseille a gasar Champions League a Faransa.

Komawarsa ta jawo hankalin jama’a ne musamman bayan wata hira da ya yi a baya, inda ya zargi Liverpool da watsar da shi bayan an ajiye shi a benci sau uku a jere, tare da cewa ba shi da kyakkyawar alaƙa da koci Arne Slot.

Sai dai daga bisani Salah ya buga wasa a matsayin wanda ya maye gurbi a wasan da Liverpool ta doke Brighton 2-0, inda ya bayar da ƙwallo aka ci.

Slot ya ce ya yi maraba da dawowar Salah, amma bai tabbatar ko zai buga wasan Marseille ba.

Salah shi ne na uku mafi yawan cin ƙwallo a tarihin Liverpool, inda ya zura ƙwallaye 250 a wasanni 421 tun bayan zuwansa daga Roma a 2017.

Sai dai tun bayan sabunta kwantiraginsa, Salah ya ci ƙwallaye biyar kacal a dukkan gasa a wannan kakar, yayin da Liverpool da ke mataki na huɗu na da tazarar maki 14 tsakaninta da Arsenal mai jan ragamar teburin Premier League.

A halin yanzu, Liverpool tana matsayi na tara a jadawalin Champions League, inda ƙungiyoyi takwas na farko kai tsaye za su tsallaka zuwa zagaye na gaba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *