Binciken CGTN: Tattalin Arzikin Sin Ya Samar Da Tabbaci Ga Tattalin Arzikin Duniya Mai Cike Da Sauye-Sauye

[ad_1]

Yawan GDPn kasar Sin ya zarce yuan triliyan 140, wanda ya karu da kaso 5 cikin dari, idan an kididdige shi bisa farashi mai dorewa. Wannan shi ne sakamakon da tattalin arzikin Sin ta samu a shekarar 2025, wanda ya ingiza bunkasar tattalin arzikin duniya dake cikin “yanayin sanyi mai tsanani”.

Sakamakon wani bincike da kafar yada labarai ta CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ta gudanar, ya nuna cewa, kusan kashi 82.6% masu bayyana ra’ayoyi, sun bayyana cewa, ci gaba mai inganci na tattalin arzikin kasar Sin ya bayar da jagoranci ga bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya.

Kazalika, yawan kudade daga hada-hadar kayayyakin shige da fice da Sin ta samu, ya zarce yuan tiriliyan 45 a shekarar 2025, wanda hakan ya ci gaba da bunkasa a cikin shekaru 9 a jere. Binciken ya kuma nuna kaso 86.6% na masu bayyana ra’ayoyin sun yi imanin cewa, babbar kasuwar Sin tana ci gaba da fadadawa da kuma inganta, wanda hakan ke samar da karin damammaki ga sauran kasashe, kuma kashi 83.6% suna ganin cewa, jerin manufofi, da matakan da aka gabatar a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, don bunkasa bude kofa bisa babban mataki, sun sake nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai goyon bayan dunkulewar tattalin arzikin duniya, kuma mai kiyaye ra’ayin bangarori daban daban. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *