Gobara ta tashi a layin ’yan canji a Tsohuwar Kasuwar Sakkwato

[ad_1]



Wutar gobara da ta tashi a safiyar Lahadi a sanadin wutar lantarki ta laƙume shaguna 50 a tsohuwar Kasuwar Sakkwato.

Wutar ta kama a layi mafi tsada a kasuwar inda ake sayar da kayan tireda da harkar canjin kuɗi da turare da sauran kayan abinci na kwali, inda ta cinye kayan miliyoyin naira wanda har yanzu ba a ƙididdige kimarsu ba.

Shugaban ƙungiyar ’yan kasuwa na Jihar Sakkwato, Alhaji Cika Sarkin Gishiri, ya ce wutar ta soma ne da misalin ƙarfe 10 na safe a ranar Lahadi ta laƙume shaguna 50 tare da cinye kaya da kuɗinsu zai kai miliyan 100, sai dai ba a samu hasarar rayuwa ba.

Alhaji Sarkin Gishiri ya roƙi gwamnatin jiha ta tallafa wa waɗanda abin ya shafa domin su ci gaba da kasuwancinsu.

Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu ya jajanta wa ’yan kasuwar da suka samu ibtila’in gobarar ya yi alƙawarin gwamnati za ta tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa..

Gwamna ya bayyana lamarin matsayin jarabawa daga Allah, kuma y yi kira ga waɗanda shagunansu suka ƙone su bar wa Allah.

“Wannan gobarar ta shafi gwamnati da dukkan al’ummar jiha, ba ta tsaya kawai ga ’yan kasuwa ba,” a cewar Gwamnan.

Ya bayyana cewa kasuwar tana cikin manyan wuraren da ake samar da kayan more rayuwa ga mutanen jiha.

Gwamnan ya ba da tabbaci ga shugabannin ’yan kasuwar cewa gwamnatinsa na da ƙudirin tallafawa ’yan kasuwa da gobarar ta shafa.

Ya roƙi Allah Ya kare aukuwar haka a gaba, ya kuma kira da ’yan tireda su cigaba da yin addu’a kan kasuwanci.

Gwamnan ya jinjina wa ma’aikatan kashe gobara na jiha da ’yan kasuwa kan ɗaukin da suka kawo aka kashe wutar ba ta tsallaka zuwa wasu shaguna ba.

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal shi ma ya yi jaje ga ’yan kasuwar ya roƙi Allah Ya kare faruwar haka a gaba.

Ya yi kira ga masu shagunan su ɗauki wannan a matsayin ƙaddara daga Allah.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *