Tsibirin Hainan Na Sin Ya Samu Bunkasar Cinikayya Karkashin Tsarin Jingine Harajin Sayayya
[ad_1]
Cikin wata guda da fara aiwatar da manufar nan ta tsarin musamman na ayyukan kwastam, a yankin cinikayya marar shinge na bakin teku, na tsibirin Hainan dake kudancin kasar Sin ko FTP a takaice, matakin ya bunkasa sayayyar kayayyaki da aka daukewa haraji.
Alkaluman da hukumar kwastam ta Haikou ta fitar a Lahadin nan, sun nuna yadda daga ranar 18 ga watan Disamba da ya gabata zuwa 17 ga watan nan na Janairu, darajar sayayyar kayayyaki da aka daukewa haraji ta kai yuan biliyan 4.86, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 693.5, karuwar da ta kai ta kaso 46.8 bisa dari kan mizanin shekara-shekara, yayin da kuma adadin masu sayayya karkashin tsarin shi ma ya karu zuwa mutane 745,000, kimanin karin kaso 30.2 bisa dari kan mizanin shekara shekara, wanda hakan ya shaida wanzuwar karsashin sayayyar.
Domin tabbatar da biyan bukatun mabanbantan masu yawon bude ido, manufar dauke haraji ta tsibirin Hainan, ta samar da sabon zagayen sauyi tun daga daya ga watan Nuwamban 2025. Kana an kara adadin jerin kayayyaki da aka daukewa harajin daga 45 zuwa 47, baya ga jerin masu cin gajiyar hakan da shi ma aka fadada, zuwa matafiya dake fita daga tsibirin, matakin da ke janyo ra’ayin karin ‘yan yawon bude ido na kasa da kasa zuwa ga yin sayayya a tsibirin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link