Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe
[ad_1]
An kammala shirin gudanar da taron lafiya karo na farko a tarihin Jihar Gombe, wanda za a fara a ranar 2 ga Oktoba.
Da yake zantawa da manema labarai wannan Larabar a Gombe, Kwamishinan Lafiya, Dakta Habu Dahiru, ya bayyana cewa, za a gudanar da taron na tsawon kwanaki biyu domin tattauna matsalolin bangaren lafiya da zummar samo mafita.
Ya ce, taron zai samu halartar manyan baki ciki har da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Remi Tinubu; Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed; Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate; tare da wasu abokan hulda, ‘yan majalisar tarayya, masana harkar lafiya, kungiyoyin farar hula da kuma kafafen yaɗa labarai.
Dakta Dahiru ya ƙara da cewa, a yayin taron, gwamnati za ta ƙaddamar da cibiyar kiran gaggawa ta lafiya da kuma tura motocin daukar marasa lafiya (ambulance), domin ba da agaji cikin gaggawa a dukkan sassan jihar.
A cewarsa, wannan sabon tsarin zai bai wa jama’a damar kiran hukumomin lafiya cikin sauri domin daukar marasa lafiya zuwa asibiti ba tare da bata lokaci ba.
“Wannan shiri zai sauya tsarin ba da agajin gaggawa a Gombe, kuma taron alama ce ta sabon babi a yunƙurin gwamnati na inganta harkokin lafiya a jihar,” in ji shi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link