Ana Ci Gaba Da Allah-wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Kasuwar Hausawa A Edo

[ad_1]

Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa (CNG), ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa ƴan kasuwar Hausawa a Ekpoma da ke gundumar Edo ta tsakiya, inda ta bayyana lamarin a matsayin wani abin da bai dace ba da zai iya ta’azzara rikicin ƙabilanci, idan ba a gaggauta magance su ba.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Litinin ta hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi, ta bayyana rashin jin daɗinta kan rahotannin da ke cewa; wasu matasa sun fatattaki ƴan kasuwar Hausawa daga kasuwar dabbobi tare da yanka akuyoyinsu, biyo bayan kashe wani matashin yankin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi.

  • Zargin Barin Almakashin Tiyata Acikin Wata Mata Ya Yi Ajalin Mutuwarta A Kano
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Watsi Da Aniyar Amfani Da Karfi Kan Iran

A cewar CNG, an ga ƴan kasuwar Hausa na tserewa daga kasuwar cikin fargaba, suna barin dabbobinsu, yayin da wasu mazauna yankin suka ci gaba da yin ɓarna ta hanyar kashe dabbobin da aka bari.

Yayin da ta ke nuna baƙin ciki da ɓacin rai da ke tattare da kisan gillar da aka yi wa matasan yankin, ƙungiyar ta jaddada cewa; ba za a amince da kai wa ƴan kasuwar da ba su ji ba, ba su gani ba, wanda hakan ya zama wani babban rashin adalci.

Charanchi ya ƙara da cewa, “Ayyukan da wasu mutane da suka ɗauki doka a hannunsu, ba na dabbanci ba ne kawai, illa dai na lalata tsarin al’ummarmu ne.” “An tilasta wa ƴan kasuwarmu tserewa, don tsira da rayukansu, sun bar dukiyoyinsu, an ci gaba da yi musu ɓarna.

Gamayyar ƙungiyoyin, ta yi gargaɗin cewa; barin irin wannan lamari ba tare da la’akari da shi ba, zai iya haifar da tashin hankali tsakanin al’umma da kuma lalata dangantakar da ke tsakanin al’ummomin da suka yi zaman lafiya a tsawon lokaci.

Ƙungiyar ta CNG, ta yi kira ga gwamnatin Jihar Edo, da ta ɗauki matakin gaggawa; don kare rayuka da dukiyoyin ɗaukacin mazauna yankin, ba tare da la’akari da ƙabila ko yare ba. Ƙungiyar ta ce, za ta ɗora wa gwamnatin jihar alhakin tabbatar da tsaron al’ummar Hausawa a Edo ta tsakiya da sauran sassan jihar.

“Al’ummar Hausawa, kamar kowace ƙabila a Nijeriya, sun cancanci zama lafiya da tsaro,” in ji Charanchi. “Ba za mu ƙara sanya ido ana kai wa mutanenmu hari da kuma ware su a wuraren da suke zama a matsayin ƴan tsiraru ba.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *