Mutfwang ya yi ta’aziyyar rasuwar malamin da ceci Kiristoci a rikicin Filato
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana alhininsa game da rasuwar Alhaji Abubakar Abdullahi, Limamin Yelwa da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a jihar.
Malamin ya yi fice a shekarar 2018 bayan da ya ceci rayukan Kiristoci sama da 262 ta hanyar ɓoye su a cikin masallaci yayin da rikici ya ɓarke a yankin.
Wannan jarumta da ya yi ta samu yabo a faɗin Najeriya da ma ƙasashen waje.
A cikin saƙon ta’aziyya, Gwamna Mutfwang ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai son zaman lafiya, wanda ya yi aiki tuƙuru wajen haɗa kan al’umma da kare masu rauni, musamman mata da ƙananan yara.
Ya ce ayyukansa sun jawo wa Jihar Filato da ma Najeriya ɗaukaka.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta zaman lafiya da fahimta tsakani mabiya addinai, tare da gina amana da haɗin kai a tsakanin al’ummar yankin.
Ya ƙara da cewa rasuwar Malam Abdullahi babban rashi ne ga iyalansa, al’ummar Yelwa da ma Jihar Filato baki ɗaya.
Ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalansa da ɗalibansa haƙuri da juriya.