‘Yan Majalisar PDP Sun Yi Allah-wadai Da Zargin Alaƙanta Gwamnan Bauchi Da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci

[ad_1]

’Yan Majalisar Wakilai na Jam’iyyar PDP daga Jihar Bauchi sun bayyana cikakken goyon baya da biyayya ba tare da tangarɗa ba ga Gwamna Bala Muhammad, bisa abin da suka kira “yaɓa masa zargin alaka da ɗaukan nauyin ayyukan ta’addanci”.

A cikin wata sanarwa da suka fitar ga manema labarai jiya a Bauchi, ƙungiyar ‘yan majalisan ta ce duk da cewa batun yana gaban kotu a halin yanzu, ya zama dole a tunatar da ‘yan Nijeriya tarihin Gwamna Bala Mohammed na bada fifiko da muhimmanta harkokin tsaro, kwanciyar hankali da ci gaban Jihar Bauchi a kowane lokaci.

  • Trump Ya Yi Barazanar Ƙaƙaba Haraji Kan Ƙasashen Da Ke Kasuwanci Da Iran
  • AFCON 2025: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kafin Karawar Nijeriya Da Morocco

“Yana da muhimmanci mu jaddada ingantaccen tarihi na Gwamna Bala Mohammed a matsayin shugaba da ya dinga sanya kwanciyar al’umma da tsaronsu da ci gaban Jihar Bauchi sama da komai,” In ji sanarwar.

Sanarwar ta samu sa hannun ’yan Majalisar Wakilai na tarayya bakwai na PDP daga Jihar Bauchi da suka haɗa da Hon. Aliyu Aminu Garu (Mazaɓar Tarayya ta Bauchi), Hon. Mansur Manu Soro (Darazo/Ganjuwa), Hon. Auwalu Gwalabe (Katagum), Hon. Adamu Hashimu Ranga (Ningi/Warji), Hon. Mohammed Dan Abba Shehu (Zaki), Hon. Bappa Aliyu Misau (Misau/Dambam), da Hon. Sani Ibrahim Tanko (Da ke wakiltar Mazaɓar Shira/Giade).

A cewar ƙungiyar, Gwamna Bala Mohammed ya yi nasarar rage ayyukan ‘yan fashi da makami a Jihar Bauchi tsawon shekaru shida da suka gabata, duk da wata matsalar tsaro da ke tasowa sakamakon makwabtakar jihar da jihohin da ke fama da matsalar fashi da makami kamar Zamfara da Katsina.

“A daidai lokacin da matsalar tsaro ta tilasta wa jama’a yin ƙaura a Arewa maso Yamma da wasu sassan ƙasar nan, Jihar Bauchi ta ci gaba da kasancewa cikin aminci kuma wurin samun mafaka, sakamakon shugabanci mai inganci da hangen nesa da kuma shirin ko ta kwana ga matsalolin tsaro,” In ji su.

‘Yan Majalisar sun kuma jaddada cewa duk da kasancewar Jihar Bauchi a yankin Arewa Maso Gabas, ta ci gaba da kasancewa babu tasirin ta’addancin Boko Haram a duk tsawon mulkin Gwamna Bala Mohammed.

“Wannan nasara ba ta zo haka nan ba. Ta samo asali ne daga manufofi na gangan, kyakkyawar haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, da ƙudurin gwamna na hana ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka samun kafar zama a jihar,” sanarwar ta ƙara da cewa.

Ƙungiyar ta bayyana zarge-zargen da ke alaƙanta gwamnan da ɗaukar nauyin ta’addanci a matsayin zargin da hankali ba zai ɗauka ba lura da azamar gwamnan na kyautata harkokin tsaro, kuma zargin ya saɓanin haƙiƙankn abin da mutanen Jihar Bauchi shaidawa na samun ingancin tsaro da kwanciyar hankali a zahirance.

“Gwamna da ya dinga hana ‘yan ta’adda samun sarari, ya kare al’umma, kuma ya tabbatar da dorewar zaman lafiya ba za a iya kiran sa mai ɗaukar nauyin ta’addanci ba ta kowace hanya,” In ji su.

Baya ga tsaro, ‘yan majalisan su haskaka abin da suka kira manyan nasarori da ba a taɓa ganin irinsu ba a fannonin ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma da walwalar jama’a a tsawon shekaru shida na mulkin Gwamna Bala Mohammed.

“Waɗannan nasarori sun fi kowace yekuwar siyasa, kuma suna bayyana ƙudurin gwamna na kyakkyawan shugabanci da mayar da hankali kan jin daɗin jama’a,” In ji sanarwar.

Ƙungiyar ‘yan majalisun PDP ta Bauchi ta yi kira ga ’yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu tare da yin nazari mai kyau, tana mai roƙon jama’a su mutunta doka da oda tare da barin gaskiya ta bayyana kanta ta hanyoyin da doka ta tanada.

“Muna da cikakken tabbacin cewa mutuncin Gwamna Bala Mohammed, tarihinsa na aiki da hidimarsa ga Jihar Bauchi za su tabbata a ƙarshe,” in ji sanarwar a ƙarshe.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *