Muhimmancin Koya Wa ‘Yan Mata Ayyukan Gida Kafin Shiga Gidan Miji


Shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantajewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu iyayen ba sa iya koya wa yaransu mata aikace-aikacen gida kamar su; Shara, wanke-wanke, wankin ‘toilet’, wankin kayan sakawa kanana, gyaran ‘Kitchen’, girki, da dai sauransu. Har sai idan auransu ya gabato sannan a lokacin za a fara kokarin koya musu.

Wannan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Ko me za a ce game da hakan?,  Ko akwai wasu matsaloli da za ta iya fuskanta a gidan aure game da hakan, musamman yadda aka koya mata a kuracen lokaci?, wadanne hanyoyi ya kamata iyaye su bi wajen koyawa yaransu mata yadda za su iya aikace-aikacen gida ba tare da sun sha wahala ba?”.

Ga dai bayannan nasu kamar haka;

Sunana Nura Garba, Karamar Hukumar Tsanyawa, Jihar Kano:

Gaskiya rashin koyawa na taimakawa wasu ne ganin kamar idan sun je gidajen su, alfarma suke wa mazajen su, ba wajibi bane, domin bata iya tun daga gida ba. Matsaloli; rashin samun kulawa da mutuntawa a wajen miji da ‘yan’uwansa, domin duk kyanki babu tsafta gaskiya ba za ki samu kyautatawa daga wajen miji ba, wani lokacin hakan ka iya jawo rabuwar aure. Hanyoyin daya kamata iyaye su bi, ya kamata duk Aiyukan da uwa take na gida ta dinga nunawa ‘yarta tama yi mata bayani, domin hakan zai saka yaran su tashi da wannan tarbiyya da aka basu, kafin harkar social media ta bata tunanin su. Shawara ga iyaye su dauka duk abin da ‘ya’yan su suka yi a waje, su ake kallo, saboda haka su yi kokarin koyawa yaran su abin da nan gaba za su yi alfahari da hakan.

Sunana Muktari Sabo, Jahun, Jihar Jigawa:

Eh, Lalle wannan abu yana faruwa kuma hakan yana samo asali ne daga yadda Iyaye suke nunawa ‘ya’yansu gata sai daga karshe kuma su fara nema musu mafita bayan lokaci ya kure. Tabbas akwai matsala domin za ta je bata iya girki da sauran aikace-aikacen gida ba, wanda hakan zai fara kawo mata matsala da mijinta musamman rashin iya girki. Kamata yayi su fara koya musu tun da wuri kadan-kadan har su koya kafin aurensu. Shawara a nan ita ce iyaye su koyawa yara ayyukan gida tun lokaci bai kure ba.

Sunana Khadija Auwal Ahmad, Koki, A Jihar Kano:

Gaskiya akwai babbar matsala, domin kuwa duk abin da ba a yi shi da wuri ba to, za a samu babbar matsala. Tun a matakin farko ya kamata ace an fara koya musu ba sai lokaci ya kure ba. Gaskiya duk iyayen da suke da irin wannan dabi’ar to, su daina domin kuwa za su Jawa kansu zagi ta hanyar cewa laifin sune basu tsaya sun nunawa yaransu abin da ya kamata ba tunda wuri.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano:

Gaskiya hakan bai dace ba. Matsala babba ma kuwa, domin har ga Allah 50% zuwa 70% zai iya sawa zaman auren ma ya ki yuwuwa. Hanyoyin suna da yawa, amma kadan daga ciki sune; idan uwa ta san me take yi to, tun daga wajen shekara 5 ya kamata a fara koyawa yara mata aikin gida irin su; wanke-wanke sharar daki wasu ma har da dan dafa abinci da sauransu. Shawarata a nan ita ce gaskiya iyaye suna kara kula sosai domin rashin iya ayyukan gida da rashin iya koyon girki a gidajen sabbin yara matan auren bana bakwai shi ne yake kara rusa auren da ba a dade da yinsa ba. Allah ya sa mu dace.

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Naija:

Yarinya tana tashi indai ‘ya mace ce, abu na farko ka fara koya mata aikace-aikacen gida, kamar ni yanzu yarana da suka tashi bana yin komai, duk su suke yi min aikace-aikacen gida, sai abin da ya zama dole yaro baya nan za ka yi. In ka koyawa yaronka komai da wuri zai ji dadi a gaba, musamman zamanin da ake ciki na sai a ga mace ta yi aure bata iya girki ba, ko ta yi eani irin aiki wanda za ka yi mamaki, ko ta yi wani irin girki da sai ka rike baki. Sanganta yaro kana ganin ba za ka iya kwabar sa ba, ba abu ne me kyau ba. Matsaloli na da yawa, musamman in ta je gidan kishiya akwai damuwa me yawa. Hanyar magancewa tun yaro na karami kafin shekara goma koya mata, yi min shara, mikon kaza, yi min jajjage, da sauransu har ya zo ya iya.

Sunana Zainab Shu’aibu, Jihar Kaduna:

Hakan na iya faruwa a ko’ina, kuma abu ne da ya zama ruwan dare a yanzu ga yara mata. Gaskiya akwai gagarumar matsala, saboda za ta rika fuskantar bakin ciki da gori daga wurin shi mijin, ko bai yi mata a farkon aure ba zai yi mata a gaba. Tun a farkon tasawar yarinyar za a fara koya mata, za a iya saka su dauko wani abun da yin wani abun, musamman shara idan sharar bata yi ba, yaron ya kara tisawa. Idan ma girki ne a kullum ta rika tayawa har ita ma ta koya ta iya, a gaba za ta gane an yi mata gata.

Sunana Alhassan Abdulrahman Bununu, Tafawa Balewa, Jihar Bauchi:

A gaskiya hakan bai dace ba saboda baso bane irin wannan kuma ba kauna ba ce ace ba a so yarinya aga ta wahala sakamakon aikace-aikace hakan zai sa su koma raini sakamakon komai yi musu ake. Tabbas kuwa akwai babban matsala sakamakon rashin sanin ina rayuwa za ta kai mu ko kuma ya za ta juya mana bamu sani ba hakan kan iya jawo mata matsala a rayuwar auranta saboda ta saba da rashin aiki. Iyaye su rika koyawa yaransu aikace-aikace tun suna yara ta hanyar saka su wanki, sharan daki ko tsakar gida da wanke-wanke.

Sunana Comr. Nr. Ibrahim Lawan Stk:

Babban kuskure shi ne rashin koyawa yara mata aikace-aikacen gida kafin ayi musu aure, ‘yan mata da dama na daukar cewa mu’amular tarayya tsakanin namiji da mace a wannan zamani shi ne makasudin so da kauna a inda wasu ke ganin cewa shi ne dalilin yin Aure. Matsalar rashin iya girki na iya haifar da rashin sinadari a cikin miya ko abinci a wani lokacin, ko kuma yawaitar sinadarin wanda kansa abinci ya lalace ko ya baci daga dandano da ya kamata ya kasance, wari sakamakon rashin tsafta na wake-wanken kayan sawa, kayan cin abinci, da bandaki wanda hakan na iya haifar da warin jiki, daki dama cikin gida wanda hakan na iya saka wa miji ya ji matarsa ta fita a ransa ta yadda zai iya dauka kowane irin mataki a kanta. Su kasance masu saka ido akan yaran su ‘yan mata domin kula da yadda suke aiwatar da aikace-aikace. Domin samun horo mai inganci da kwarewa, akan aikace-aikacen gida.

Sunana Aisha T. Bello Daga Jihar Katsina:

Wasu gaskiya suna kuskure, saboda sai ka ga yarinya tun tana karama bata komai a gida sai bacci har ta girma saboda ta saba bata komai. Matsala; iyaye za su aurar da mace bata iya girki ba. Na taba ganin wadda bata iya girki ba har mai aiki aka kawo mata, amma bata iya ba, ina amfani haka. Tun yariya na karama mu yi kokarin koyar da ita aikin gida musamman girki. Idan muka koyawa yaran mu aikin gida, za mu ji dadi musamman in mun yi musu aure.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *