Tsohon ɗan wasan Arsenal Guendouzi zai koma Fenerbahce

[ad_1]



Tsohon ɗan wasan tsakiya na Arsenal, Matteo Guendouzi, na dab da komawa ƙungiyar Fenerbahce ta Turkiyya daga Lazio, kamar yadda kulob ɗin ya sanar.

Guendouzi mai shekaru 26, ya murza leda a Arsenal tsawon shekaru biyu, sannan ya buga wa Hertha Berlin da Marseille kafin komawarsa Lazio a shekarar 2023.

Rahotanni na nuna cewa Fenerbahce na shirin sayen ɗan wasan kan kuɗi Yuro miliyan 30, inda ake sa ran zai sanya hannu kan kwantaragin shekaru biyar da rabi.

A sanarwar da ta wallafa a shafukan sada zumunta, Fenerbahce ta ce tana ci gaba da tattaunawa da Guendouzi da kulob ɗinsa domin kammala cinikin, tare da gayyatarsa zuwa Istanbul domin gwajin lafiyarsa.

Guendouzi, wanda ya buga wa ƙasar Faransa wasanni 14, kulob ɗinsa na gaba Fenerbahce na matsayi na biyu a teburin gasar lig, inda take baya da Galatasaray da maki uku kacal.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *