Za Mu Baza Ƙarin Jami’anmu A Faɗin Nijeriya Don Samar Da Tsaro – Sojoji
Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce za su ƙara ƙaimi domin hana yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a jihar Neja da sauran sassan Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne bayan harin da wasu mahara suka kai Kasuwan Daji a Jihar Neja a ƙarshen makon da ya gabata, inda suka kashe sama da mutane 40, tare da sace wasu, sannan suka ƙone kasuwar.
- Sojoji Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
- AFCON 2025: Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Algeria A Wasan Kwata Fainal
Laftanar Janar Shaibu ya ce sojoji za su mayar da hankali wajen aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa na murƙushe ayyukan ‘yan bindiga, kamar yadda kamfanin dillancin labarai (NAN) ya ruwaito.
Bayan harin, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su yi duk mai yiwuwa domin ceto mutanen da aka sace.
“Za mu baza jami’an tsaronmu a sassan ƙasar nan domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka a Nijeriya,” in ji Babban Hafsan Sojin Ƙasa.