’Yan sanda sun ceto yara huɗu da aka sace a Nasarawa
[ad_1]
Jami’an ’yan sanda sun samu nasarar ceto wasu yara huɗu da ake zargin an yi garkuwa da su a Jihar Nasarawa.
Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa yaran sun ɓace ne tun ranar 31 ga Disamban 2025, a Ƙaramar Hukumar Karu, lamarin da ya sa suka fara bincike.
“Bayan samun bayanan sirri, jami’an ’yan sanda daga Nasarawa da Babban Birnin Tarayya suka gano maboyar masu laifin, inda suka ceto yaran lafiya lau.”
Binciken farko ya nuna cewa wasu mutane biyu — Abraham Asoje mai shekaru 28 da Joy Bolaje mai shekaru 29 — ne ake zargin sun sace yaran kuma suka tsare su.
’Yan sandan sun ce an mayar da yaran hannun iyayensu, yayin da ake ci gaba da farautar sauran mutanen da ke da hannu a lamarin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar wa al’umma aniyar rundunar ta kare rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma shawarci iyaye da masu kula da yara su ƙara sa ido, tare da kira ga jama’a su riƙa kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link