Yara biyar sun rasu bayan katanga ta danne su a Maiduguri
Yara biyar sun mutu, wani ɗaya ya jikkata sakamakon faɗuwar katangar wani gida a kansu a unguwar Bulumkutu da ke Maiduguri, Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare ranar Lahadi, inda katangar ya danne ƙananan yara shida da ke wasa a kusa da wurin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda a Jihar Borno, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Mun samu rahoto daga DPO na Bulumkutu cewa katangar ya rushe kan yara shida. Abin takaici, yara biyar, duk ƙasa da shekaru 16, sun rasu, yayin da ɗaya ya jikkata kuma yanzu haka yana karɓar magani a asibiti,” in ji shi.
Ya ce an fara gudanar da bincike don gano musabbabin rushewar katangar.
Daso ya yi kira ga jama’a da su kula da ingancin gine-gine da tsaron yara.
“Muna kira ga jama’a da su kula da tsaron gine-gine, su yi amfani da ingantattun ƙa’idojin gine-gine, kuma su riƙa kula da ’ya’yansu sosai,” in ji shi.