Sarkin Hausawan Ibadan ya rasu

[ad_1]



Allah iya yi wa Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Dahiru Zungeru, rasuwa.

Sarkin ya rasu ne da yammacin yau Litinin a gidansa da ke Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Marigayi Alhaji Ali Dahiru Zungeru, wanda ya hau karagar mulki shekaru huɗu da suka gabata, ya sha fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa.

Aminiya ta ruwaito cewa jim kaɗan bayan sanar da rasuwar, wasu manyan hakimai da suka haɗa da Jarman Ibadan, Alhaji Danjuma Yakubu, da Sardaunan Ibadan, Alhaji Husaini Kabiru, suka garzaya ofishin Gwamnan Jihar Oyo da Fadar Olubadan na Ibadan domin sanar da su labarin rasuwar Sarkin Hausawan.

Manyan hakiman sun shaida wa Aminiya cewa gobe Talata da misalin ƙarfe 10 na safe ne za a suturta Sarkin Hausawan Ibadan a cikin gidansa da ke Unguwar Sabo, kamar yadda aka yi wa kakanninsa da iyayensa a baya.

Sun kuma tabbatar da cewa ofishin Gwamnan Jihar da Fadar Olubadan sun yi alkawarin tura wakilansu domin halartar jana’izar marigayin.

Aminiya ta ce a halin yanzu Unguwar Sabo, matsugunnin Hausawa a birnin Ibadan, ta fara cika da ɗimbin jama’a maza da mata daga sassa daban-daban na garuruwa da ke kewaye da Ibadan, domin halartar jana’izar gobe Talata.

Haka kuma, an ga shaguna da runfunan ’yan kasuwa da dama a Unguwar Sabo, inda suka yi ado da alamun jimami domin nuna alhininsu ga wannan babban rashi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *