AFCON: Tunisia Ta Kori Kocinta Bayan Ficewa Daga Gasar
[ad_1]
Daga Rabilu Sanusi Bena
Hukumar kwallon kafa ta kasar Tunisia ta raba gari da kocin babbar tawagar kwallon kafa ta kasar Sami Trabelsi bayan rashin nasarar da tayi a hannun Mali a bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan zagayen 16 da suka buga ranar Asabar, ficewa daga gasar ya janyo suka daga yan kasar wadanda ke ganin ba a wannan matakin ya kamata ace kasar tasu ta fice daga gasar ta bana ba.
Hukumar kwallon kafa ta Tunisia ta tabbatar da korar Sami a ranar Lahadi, kasa da kwana daya bayan da Mali ta fitar da Tunisia a zagaye na 16, wasan ya kare da ci 1-1 bayan karin mintuna 30 da alkalin wasa yayi, amma Mali ta samu nasara a bugun Fenarati da ci 3-2, Hakan ya janyowa yan Arewacin Afirika din ficewa daga gasar, a cikin wata gajeriyar sanarwa, hukumar ta bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne ta hanyar amincewa da juna tsakaninta da Trabelsi da sauran masu horar da tawagar.
“Kwamitin zartarwa ya yanke shawarar dakatar da dangantakar kwantiragin dake tsakaninta da Sami Trabelsi da kuma dukkan masu horarwa na tawagar” in ji wani rubutu da hukumar CAF ta ce ta tsinto a shafint FTF na yanar gizo, korar ta biyo bayan cece-kuce tsakanin magoya baya da masu sharhi kan kwallon kafa, wadanda da yawa daga cikinsu sun bayyana Tunisia a matsayin kasar da ka iya lashe gasar da ake cigaba da bugawa a Morocco.
[ad_2]
Source link