Yadda Ake Boga

[ad_1]

Daga Bikiis Tijjani Kasim

Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.

A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake hada Boga.

Abubuwan da za a tanada:

Nama nikakke, Biredin Boga, Albasa, Garin tafarnuwa, Gishiri, Barkono, Kayan yaji, Mai, Kabeji, Tumatir, Kukumba, Kyacuf ko mayanus, Cuku idan ana so, Kwai 1 shima ba dole bane.

Yadda ake hadawa:

A zuba nikakken nama a kwano, sannan a yanka albasa guda daya a ciki, sai a zuba garin tafarnuwa kamar cokali daya, gishiri daidai gwargwado, barkono kadan da kayan yaji, sai a gauraya sosai, sannan a rika murzawa sai a yi faifan nama (Patty).

A zuba mai kadan a kwanon suya, a soya patty har ya yi ja sannan a juya saman ma yayi ja.

A yanka Biredin Boga gida biyu, a dan gasa shi kadan haka, sannan a shafa kyacuf ko mayanus a cikin Biredin.

Sai a yanka Kabeji sirara sannan a jera, a yanka tumatir rawun a jera, sai a yanka kukumb a jera, sai patty, a saka cuku idan ana so.

A rufe da saman Biredin, Boga dinki ya kammala!

Ana iya ci da soyayyen dankali ko abin sha.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *