AU Ta Yi Maraba Da Shawarar Sin Da Pakistan Kan Dawo Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya
[ad_1]
A yau Jumma’a, kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta yi maraba da shawarar hadin gwiwa ta Sin da Pakistan mai matakai biyar game da tinkarar kalubalen zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake fuskanta a yankin Gulf da Gabas ta Tsakiya.
Shugaban hukumar AU, Mahmoud Ali Youssouf, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, shawarar ta kawo gudummawa mai muhimmanci kuma a kan lokaci ga kokarin kasa da kasa da ake yi na saukaka tashe-tashen hankula da kuma zurfafa bin hanyoyin siyasa da diflomasiyya.
Youssouf ya sake jaddada matukar damuwarsa kan ci gaba da karuwar tashin hankali a yankin Gulf da Gabas ta Tsakiya. Ya kuma jaddada cewa, rikicin ya riga ya haifar da ji a jika a duk duniya, ciki har da bangaren tsarin samar da makamashi, da na abinci, da rashin kwanciyar hankali ga tattalin tattalin arziki, musamman a Afirka, wadda tuni dama tana fuskantar dimbin kalubale da suke cakudewa da juna. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link