BYD Ya Zarce Tesla A Yawan Sayar Da Motoci Masu Aiki Da Lantarki A 2025
Katafaren kamfanin kirar motoci masu aiki da lantarki na kasar Sin wato BYD, ya sayar da adadin motocin lantarki kimanin miliyan 2.26 a shekarar 2025, adadin da ya zarce miliyan 1.63 da kamfanin Tesla ya sayar a shekarar ta bara.
Wasu alkaluma na kamfanin BYD, sun ce adadin ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi da kamfanin ya sayar a bara, ya kai kimanin miliyan 4.6. Kamfanin BYD ya ce ya fadada kasuwarsa a kasar Sin, tare da kara yawan sayar da motocinsa a ketare. A Turai kuma, kasuwancin kamfanin na kara bunkasa, kuma yana mayar da hankali ga kasuwannin Latin Amurka da na kudu maso gabashin Asiya.
A daya bangaren, BYD ya himmatu wajen yalwata samar da hajoji a sassan da yake gudanar da hada-hada, inda masana’antarsa dake kasar Brazil ta fara aiki gadan-gadan a shekarar da ta gabata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)