’Yansanda Sun Kama Mutane 2 Kan Sace Matan Aure A Kaduna

[ad_1]

Rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutane biyu da ake zargin su da sace wasu matan aure biyu a jihar.

Masani kan harkar tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa X a ranar Laraba.

  • Ko Za A Yankani Ba Zan Koma APC Ba – Gwamnan Bauchi
  • Me Ya Sa Kasar Sin Ta Jawo Hankulan Masu Zuba Jari Daga Kasashen Waje A 2025?

Ana zargin waɗanda ake tuhuma sun sace matan sannan suka riƙe su na wani lokaci kafin daga baya su sake su.

Bayan sako matan, sun taimaka wa hukumomin tsaro wajen gano waɗanda ake zargin.

Daga baya, matan sun yadda su gana da waɗanda ake zargin a wani waje a Kaduna.

Dangane da bayanan sirri da aka samu kafin hakan, ‘yansanda suka je wajen suka kama waɗanda ake zargin.

Yanzu haka, waɗanda ake zargin suna hannun ‘yansanda, kuma ana ci gaba da bincike don gano ƙarin bayani ko akwai wasu da suke da hannu laifin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *