Diflomasiyyar Sin Ta Ciri Tuta!

[ad_1]

’Yan kwanaki bayan shiga sabuwar shekarar nan ta 2026, duniya na ci gaba da fuskantar yanayi na tangal-tangal, kana muna ta jin labarai marasa dadi na tashe-tashen hankula a wasu sassan duniya daban daban. To sai dai kuma duk da haka, a daya bangaren, muna iya cewa mun shiga sabuwar shekarar ta bana da kyakkyawan fatan kyautatuwar lamura, musamman ganin yadda salon diflomasiyyar kasar Sin ke kara samar da tagomashi ga cundayar al’ummun duniya bisa mutunta juna, da yunkurin kare moriyar juna, da adawa da matakan kashin kai, ko keta hurumin ’yancin kasashe na mulkin kai da kiyaye yankunansu.

Mun ga yadda manyan jami’an Sin suka bude shekarar da ziyartar kasashen ketare da dama, domin sada zumunta, da kara yaukaka fahimtar juna, ciki har da ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai kasashen Habasha, da Tanzania da Lesotho dake nahiyar Afirka. Ziyarar da ta kasance karo na 36 a jere da ministan wajen kasar Sin ke zuwa kasashen Afirka a duk farkon shekara. Ta kuma zo a gabar da ake cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Masharhanta na cewa, wannan ziyara ta alamta yadda kasar Sin ta dukufa wajen zurfafa kawance bisa adalci, da daidaito, da martaba juna, da burin cimma moriya tare. Ta hanyar aiwatar da matakai na zahiri, kasar Sin ta ci gaba da ingiza daidaito, da karsashi ga ci gaban duniya duk da tarin kalubale da ake fama da su.

A kurkusa ma, kasar Sin na kara kyautata cudanya, da zumunci tare da makwaftanta, kamar dai yadda muka ga kokarin kasar na zurfafa tattaunawa da kasashe irin su Pakistan, da Koriya ta kudu, da nufin haifar da karin daidaiton alakar makwaftaka, da aminci da bunkasa hadin gwiwa.

Har ila yau, yayin da kasashe da dama ke shan radadin karin harajin fito daga matakan kasar Amurka, a nata bangare kasar Sin ta bullo da manufar janye daukacin harajin kwastam kan hajojin dake shiga kasar daga kasashen Afirka dake da huldar diflomasiyya tare da ita, wanda hakan ke kara shaida kwazon kasar Sin na tallafawa, da goyon bayan muradun kasashe masu tasowa na samun ci gaba cikin lumana.

Yayin da ake ganin yunkurin wasu manyan kasashen duniya na kafa tsarin danniya da babakere, da kulla kawancen mayar da wasu sassa saniyar ware, a nata bangare kuwa, kasar Sin ta dukufa ne wajen shawo kan kalubalolinta na cikin gida, da kuma raba damammakin ci gabanta mai inganci ga sauran sassan kasa da kasa, karkashin salon diflomasiyyar ta dake cike da fatan cimma nasara cikin lumana, da gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil’adama. Salon diflomasiyyar da ke shan jinjinawa da goyon baya daga dukkanin kasashe masu fatan a “gudu tare a tsira tare”!(Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *