’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu

[ad_1]



Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama wasu mutane tara da ake zargi da shirin yin garkuwa da kansu tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 7.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce waɗanda ake zargin na da hannu a cikin shirin zamba na Ponzi, kuma ɗaya daga cikin tawagarsu ya shirya da wanda ake zargin ya samu kuɗin fansa daga abokan aikinsu.

An kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin mai suna Suleiman Dauda a Minna babban birnin jihar, inda daga bisani ya ambaci wasu mutum takwas da ake zargin yayin da ’yan sanda ke yi musu tambayoyi.

“A ranar 2 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 10 na dare, an samu rahoto a yankin Tudun-Wada na wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane a kusa da unguwar Mandela da ke Minna, sannan kuma an kira shi ta wata baƙuwar lambar wayar salula ana neman kuɗin fansa Naira miliyan 7.

“A cikin binciken da ake yi, a ranar 3  ga Satumba  2025, an kama wani wanda ake zargi mai suna Suleiman Dauda da laifin aikata laifin, kuma bisa ga tambayoyi, an kama wasu mutum takwas a unguwar Mandela.

“A binciken da aka yi, an ƙwato katin wayar salula SIM guda 21 da satifiket 29 a hannun Suleiman, bisa zargin cewa yana yin rijistar katin SIM ne, ya kuma yarda cewa lambar waya salula  da ake neman kuɗin fansa ya ba wanda aka aka yi garkuwan da shi.”

Duk da haka ya bayyana cewa, “Binciken da aka yi ya nuna cewa, waɗanda ake zargin sun fito ne daga wurare daban-daban a ciki da wajen jihar suna gudanar da shirin zamba na Ponzi, kuma an gano cewa ɗaya daga cikin tawagarsu ya shirya da wanda ake zargin ya karɓi kuɗin fansa daga abokan aikinsu.

Abiodun ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike da nufin ganowa tare da cafke wasu, yana mai cewa waɗanda ake zargin an gurfanar da su a gaban kotu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *