Wang Yi: Sin Babban Ginshiki Ce Ga Ci Gaban Duniya Duk Da Matsalolin Da Ake Fuskanta

[ad_1]

A yau Talata 30 ga Disamba, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a taron bita kan yanayin kasa da kasa da kuma diflomasiyar Sin na shekarar 2025, ya bayyana cewa, a wannan shekara, ci gaban tattalin arzikin duniya ya nuna sanyin jiki, yayin da manufar bangaranci da kariyar cinikayya suka kunno kansu, kuma ci gaban kowace kasa yana fuskantar babban kalubale.

Tattalin arzikin Sin ya ci gaba da tafiya ba tare da tangarda ba duk da matsin lambar da take fuskanta, yana kuma ba da goyon baya ga duniya bisa karfin juriya da wadataccen kuzari. Sannan yana samar da damammakin kasar ga duniya ta hanyar bude kofarta ga kasashen waje, ciki har da budewa ta bangaren kashin kai. Gudunmawar Sin ga ci gaban tattalin arzikin duniya ta ci gaba da kasancewa a kusan kashi 30%, wadda ta fi jimillar ta kasashen G7, ta zama babbar ginshiki mai kara wa ci gaban duniya kwarin gwiwa don magancewa da fita daga matsaloli da dimbin kalubale.

Game da dangantakar Sin da Amurka, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Amurka dole ne su nemi hanyar warware damuwar kowane bangare bisa tushen daidaito da mutunta juna da kula da moriyar juna, su kuma nemi madaidaiciyar hanyar mu’amala tsakaninsu. Ayyukan ci gaban dangantakar Sin da Amurka a wannan shekara sun nuna cewa, idan Sin da Amurka suka hada kai, dukkansu biyu suna amfana, amma idan suka yi gaba da juna, ba shakka dukkansu za su yi asara. Ba za a iya yin mu’amala bisa girman kai ba, kuma ba a yarda da daukar fuska biyu ba. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *