’Yan ta’adda sun sace mutane 50, sun tashi kauyuka 21 a Kogi




’Yan bindiga sun kashe mutane kusan 30, suka sace wasu 51 tare da tarwatsa kauyuka 21 a hare-haren da suken kaiwa a yankin Bunuland da ke Karamar Hukumar Kabba/Bunu a Jihar Kogi.

Shugabannin al’ummar Bunuland sun bayyyana wa wakilinmu a ranar Talata a taron manema labarai da aka gudanar a Lokoja, ta bakin shugaban Kungiyar Ci-gaban Al’uummar Bunu (BDA), Fasto Kokawole Johnson Folorunshon, tare da sakataren ƙungiyar, Kwamred Durowaye Ayo.

Folorunshon ya ce, “Mutanen kauyuka 21 daga cikin 38 sun bar ƙasarsu ta asali; mutane 30 sun rasa rayukansu; fiye da 51 suna hannun ’yan bindiga, ciki har da 37 da aka yi garkuwa da su a cocin ECWA a Ayetoro Kiri kwanan nan.”

Ya ci gaba da cewa ya ce Bunuland, wacce al’umma ce mai zaman lafiya da ke tsakiyar Najeriya, yanzu tana fuskantar babbar matsalar tsaro sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka mamaye yankin.

“Ana kai wa manoma hari a gonakinsu; ana yin garkuwa da matafiya a kan manyan hanyoyi; mata, yara da tsofaffi suna gudun hijira daga gidajensu na asali saboda tsoro.

“Kauyuka gaba ɗaya suna ƙara zama kufai; wannan ba matsalar cikin gida ce kawai ba. Matsalar jin kai ce kuma barazana ga rayuwar al’umma.

“Duk da ƙoƙarin hukumomin gwamnati, girma, yawan da kuma ci gaba da hare-haren nan sun nuna cewa matakan da ake ɗauka ba su isa ba.

“Al’ummomi da dama suna jin ƙara zama cikin haɗari da tsoro, kuma amincewar jama’a da gwamnati tana ƙara raguwa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa lamarin da ya fara da hare-hare na bazata yanzu ya rikide zuwa tashin hankali na dindindin, wanda ya haɗa da kisa, garkuwa da mutane, hare-haren ta’addanci da kuma tilasta wa jama’a barin gidajensu.

Shugaban BDA ya ƙara da cewa: “Idan mutane suka rasa tsaro, sun rasa komai – mutunci, rayuwa, al’adu da makoma.”

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Dattawan Bunu (BEF), Olu Obafemi, wanda aka wakilta da Elder Andrew Owonilepa, ya goyi bayan jawabin shugaban BDA, yana mai jaddada cewa matsalar da ta shafi al’ummarsu na buƙatar taimakon Gwamnatin Tarayya, jiha da ƙaramar hukuma, tare da gudunmawar kamfanoni da ’yan ƙasa.

Ya ce: “Manoma ba sa iya shiga gonakinsu, mutanenmu sun bar ƙasarsu ta asali, kuma baƙi sun mamaye gonaki suna shuka amfanin gona, suna sayar da shi gare mu. Muna buƙatar taimakon kowa.”

Haka kuma, shugaban ɗaliban Bunu na ƙasa, wanda shi ne jagoran matasan Bunuland, Kwamred Daniel Friday Aiyegboka, tare da shugabar mata ta Bunuland, Misis OluwaBumi Aromiyo, sun bayyana cewa jama’a suna yin hijira da yawa saboda tsananin rashin tsaro a yankin.

“A taimaka mana, jama’a suna yin hijira ba, ’ya’yanmu sun bar makarantu. Ba za mu iya rayuwa cikin kwanciyar hankali ba muddin ’ya’yanmu ƙasa da shekaru 8 da kuma tsofaffinmu sama da shekaru 80 suna cikin daji.”




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *