NNPP Ta Kori Shugabanta Na Kano, Dungurawa, Kan Zargin Saɓa Dokokinta

[ad_1]

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta kori shugabanta, Hashimu Dungurawa, kan zargin aikata rashin ɗa’a.

Shugabannin Gargari a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ne, suka yanke wannan hukunci a taronsu, makonni biyu bayan Dungurawa ya sake zama shugaban jam’iyyar.

  • Ɗaliban Nijeriya Sun Nemi A Dakatar Da Dokor Haraji
  • Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso

Shugabannin sun ce an kore shi ne saboda haifar da rarrabuwar kawuna a jam’iyya, tayar da rikici, rashin biyan kuɗin jam’iyya, da yin maganganu marasa ladabi ga Gwamnan Jihar Kano.

Takardar hukuncin ta bayyana cewa ayyukansa sun haifar da naƙaso ga haɗin kai da ci gaban jam’iyyar, kuma an ɗauki matakin korarsa don samar da zaman lafiya.

Sun aike takardar hukuncin zuwa ofisoshin jam’iyya na ƙasa, jiha, da ƙaramar hukuma, da kuma jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Shugabannin sun ce an kore shi ne domin hana sauran mambobi karya dokokin jam’iyyar, sannan sun sake tabbatar da biyayya ga jagoran NNPP da goyon bayansu ga Gwamna Yusuf.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *