Binciken CGTN: Bai Wa Yankin Taiwan Makamai Tamkar Sayar Da Yankin Ne Da Rusa Shi

[ad_1]

Amurka ta sake gabatar da shirin sayar da makamai ga yankin Taiwan na kasar Sin. Shirin sayar da makaman, wanda ya kai na sama da dalar Amurka biliyan 11, ya hada da na’urorin tsarin makamai masu yawa da za a iya kai hari da su a zahiri, lamarin da ya karkato da hankulan kasashen duniya da kuma fadada nuna damuwa kan halin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan.

Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a na duniya da CGTN ta gudanar ya nuna cewa kashi 90 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, yunkurin da mahukuntan Taiwan ke yi mai hadari wajen gaggauta samar da karfin soji ga yankin Taiwan ya jefa mazauna tsibirin zuwa gabar abkawa cikin yaki.

Tun lokacin da Lai Ching-te ya hau karagar mulki, ya kara hanzarta samar da karfin soji ga Taiwan, yana neman ‘yancin kai ta hanyar karfin tuwo. Mahukuntan Taiwan sun yi alkawarin kara kashe kudaden tsaro zuwa kashi 5 cikin dari na yawan alkaluman tattalin arziki (GDP) na yankin nan da shekarar 2030, ko da kuwa hakan zai iya tagayyara “arzikin Taiwan,” da kara gurgunta rayuwar jama’a da ci gaban tattalin arziki a tsibirin.

A cikin binciken, kashi 81.1 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyin sun yi imanin cewa, al’adar da mahukuntan Taiwan suka runguma ta sadaukar da muradun Taiwan na dogon lokaci domin samun moriyar siyasa na gajeren lokaci ta kawo cikas ga bunkasar tattalin arziki da ci gaban yankin. A halin da ake ciki kuma, kashi 87.7 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun ce, matakin da mahukuntan Taiwan suka dauka ya haifar da babbar barazana ga kwanciyar hankali da kuma muradun al’ummar Taiwan. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *