Ƙasashen Afirka Sun Fara Neman Man Fetur Daga Nijeriya, Dangote Ya Ƙara Farashi
[ad_1]
Matatar man Dangote ta fara fuskantar buƙatar man fetur mai yawa daga ƙasashen Afirka. Hakan na zuwa bayan rikicin Amurka da Isra’ila kan ƙasar Iran ya katse hanyoyin samar da mai.
Kamfanin ya ce ƙasashe kamar Afirka ta Kudu da wasu sun nemi kayayyaki a wurinsa, A lokaci guda, ya ƙara farashin Fetur daga N1,175 zuwa N1,245 kan kowace lita.
- Dangote Da GCL Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Masana’antar Taki A Habasha
- Matatar Dangote Ta Sake Ƙara Farashin Fetur Zuwa ₦1,175
A sanarwar da ya fitar, ya jaddada cewa tashin farashin ya biyo bayan matsin lambar siyasar duniya da bangaren makamashi ke fuskanta. Ya kuma tabbatar da cewa sabon farashin zai fara aiki daga tsakar daren 21 ga Maris, 2026.
Rahoton ya nuna farashin mai a bakin teku ya tashi zuwa N1,606,518 kan kowace ton. Hakan ya biyo bayan hauhawar farashin ɗanyen mai da tsadar sufuri a duniya.
Ana sa ran ƙarin zai shafi kasuwar cikin gida, inda masu sayarwa za su ƙara farashi. Wannan na nuna kasuwar mai a Najeriya na ci gaba da dogaro da yanayin duniya har yanzu wajen yanke farashi.
[ad_2]
Source link