Shettima da Zulum sun ziyarci waɗanda harin bam ya rutsa da su a Maiduguri
[ad_1]
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tare da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun kai ziyarcu waɗanda suka jikkata sakamakon harin ƙunar baƙin wake a wani masallaci a Jihar Borno.
An kwantar da waɗanda suka jikkata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) da kuma Asibitin Ƙwararru na Jiha da ke Maiduguri.
A yayin ziyarar, Mataimakin Shugaban Ƙasa da gwamnan sun jajanta wa waɗanda abin ya shafa.
Harin ya faru ne a ranar Laraba, yayin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya shiga Masallacin a asirce tare da tayar da bam.
Harin ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, yayin da wasu 32 suka jikkata.
Da yake magana da ’yan jarida, Shettima ya ce sun je Maiduguri ne a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa da al’ummar Jihar Borno.
Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kawo ƙarshen ta’addanci da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.
Gwamna Zulum ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Borno wajen tallafa wa ayyukan tsaro na Gwamnatin Tarayya.
Ya ce gwamnatin jihar na aiki dare da rana domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Tawagar ta samu bayani daga Daraktan Cibiyar Jinya ta Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana cewa an sallami da dama daga cikin waɗanda suka jikkata bayan samun sauƙi.
Ya ƙara da cewa sauran na ci gaba da samun kulawa yadda ya kamata, sai dai mutum ɗaya har yanzu na cikin mawuyacin hali.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link