Jama’ar gari sun kama ’yan bindiga 3 a Kastina

[ad_1]



Mutanen gari sun kama mutum uku da ake zargin suna da hannu a harin da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Ƙadisau da ke Ƙaramar Hukumar Faskari da ke Jihar Katsina.

Al’ummar yankin ne suka kama mutanen suka damƙa su ga jami’an tsaron al’umma na jihar domin gudanar da bincike.

Yankin Ƙadisau da kewaye ya sha fama da hare-haren ’yan bindiga waɗanda suka kashe mutane da dama suka jikkata wasu tare da sace dabbobi masu yawa.

Na baya-bayan nan shi ne wanda mahara suka kashe mutane uku suka yi garkuwa da mata biyar sannan suka yi awon gaba da dabbobi da ba san adadinsu ba.

Bidiyon binciken da wakilinmu ya samu ya ga jami’an tsaron suna yi wa mutanen da ake zargin— waɗanda ’yan asalin ƙauyukan Kadisau, Wasani da Maigora ne—tambayoyi.

Ɗaya daga cikinsu ya amsa cewa da shi aka kai hari a ƙauyukan Ƙadisau Kadisau, Unguwar Zango, da kuma Kanawa.

Ya kuma shaida wa masu bincike cewa shi ne ya kashe wabi mai suna Mai Soni a harin Ƙadisau, saboda mutumin ya gane shi.

Da yake jawabi cewa shi mai safarar makamai ne, ya bayyana cewa ’yan bindigar da Bello Turji ke jagoranta ne suka kai hari a Ƙadisau.
A cewarsa, Bello Turji, na gudanar da ayyukan ta’addancinsa yankunan Maigora da ke Faskari Dajin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Na biyun kuma ya shaida wa masu bincike cewa yana safarar kayan abinci da man fetur da sauransu ga wani jagoran ’yan bindiga mai suna Malam.
Baya ga haka da shi aka kai hare-hare a kauyuƙan Wasani da Raudama, da kuma Unguwar Gizo, inda aka kashe mutane `0 aka kuma sace wasu da dama tare da dabbobi.

Na ukun da ake zargi ya amsa cewa yana kai wa Malam man fetur da kayan abinci da lemon kwalba da kayan aikin gona.
Ya kuma shaida musu cewa yana da alaƙa da wani jagoran ’yan bindiga mai shan Auwali, wanda yake kai masa kaya da sauran buƙatu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *