Sin Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Bunkasa Tsimin Makamashi Da Rage Fitar Da Hayakin Carbon
Manyan jami’an gwamnatin kasar Sin sun alkawarta shirin kasar na ci gaba da bunkasa tsimin makamashi, da rage fitar da hayakin carbon mai dumama yanayi.
Jami’an ciki har da mataimakin firaministan kasar He Lifeng, da wakilan ma’aikatu da hukumomin kasar sun sha alwashin ne a jiya Laraba, a wani bangare na taron zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar dake gudana yanzu haka.
Yayin zaman, membobin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin sun tattauna game da wani rahoto mai nasaba da sanya ido, da aiwatar da dokar tsimin makamashi, sun kuma kaddamar da taron tuntuba, wanda ya samu halartar shugaban zaunannen kwamitin na majalisar wakilan jama’ar kasar Zhao Leji.
Yayin da yake tsokaci a zaman na jiya, mataimakin firaministan kasar He Lifeng, ya alkawarta cewa, Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakai daban daban na kyautata samarwa, da cin gajiyar makamashi, tare da karfafa tabbacin kaiwa ga kololuwar fitar da hayakin carbon, da rage fitar da shi, da kuma gaggauta sauya akala zuwa cikakken tsarin samar da ci gaban tattalin arziki, da zaman rayuwar al’ummun kasar Sin ba tare da gurbata muhalli ba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)