‘Yansanda Sun Kama Mutane 5 Da Ake Zargin ‘Yan Bindiga Ne A Kano.


Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama mutane biyar da ake zargi da garkuwa da mutane da satar shanu a wani samame da rundunar ta yi bayan samun bayanan sirri a kananan hukumomin Kiru da Tsanyawa na jihar.

‘Yansandan sun ce, an kai samamen ne a ranar 14 ga Disamba, 2025, wanda jami’an rundunar yaki da garkuwa da mutane ta rundunar da sauran rundunonin tsaro suka kai bayan bayanan sirri da aka samu.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda (PPRO), CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Alhamis, an kama mutane hudu daga cikin wadanda ake zargin a Rahma Round da ke karamar hukumar Kiru bayan zagaye yankin da ‘yansanda suka yi a bisa umarnin Kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori.

“Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Shafiu Ibrahim, mai shekaru 25, daga kauyen Auchanawa, karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna, ya amsa cewa shi mamba ne na wata kungiyar masu garkuwa da mutane da kuma hannu a jerin hare-haren satar shanu,” in ji sanarwar.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *