Sin Ta Bukaci Amurka Da Kada Ta Aiwatar Da Munanan Tanade-tanade Masu Alaka Da Sin A Kudirin Dokar Manufofin Tsaro
[ad_1]
Kasar Sin ta yi kira da babbar murya ga Amurka da ta yi watsi da ra’ayin cin moriya da faduwar wani, da nuna son zuciya, da kuma kauce wa aiwatar da munanan tanade-tanade masu alaka da kasar Sin a cikin kudirin dokar manufofinta na tsaro.
Mai magana da yawun kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ya bayyana hakan a yau Alhamis cewa, yayin da yake mayar da martani ga Amurka game da “kudirin dokar lisafin kudi kan harkokin tsaron kasa na shekarar 2026” da aka rattaba wa hannu a kwanan baya.
Mai magana da yawun, Xu Dong ya bayyana cewa, wannan kudiri ya ci gaba da nuna batun dakile kasar Sin, da wuce gona da iri kan “barazanar kasar Sin”, da yin katsalandan mai muni a harkokin cikin gidan kasar Sin da kawo cikas ga manyan muradun kasar Sin. Kana ya ce, kasar Sin tana nuna matukar rashin gamsuwa da kuma adawa da hakan.
Xu ya kara da cewa, ana sa ran Amurka za ta kalli ci gaban kasar Sin da dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka a bisa turbar gaskiya da kaifin hankali, da yin aiki tare da kasar Sin bisa alkibla daya, da hada karfi da karfe wajen aiwatar da muhimman daidaito da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron da suka yi a birnin Busan. Kazalika, ya ce, idan Amurka ta nace kan bin turbar kanta ita kadai, kasar Sin za ta dauki kwararan matakai bisa doka, domin kiyaye ikon mulkin kan kasarta da tsaro, da kuma muradunta. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link