Sin Ta Yi Martani Kan Shirin TikTok Na Kafa Kamfanin Hadin Gwiwa Tare Da Masu Zuba Jari Na Amurka
[ad_1]
Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin He Yongqian ta ce, gwamnatin Sin na fatan kamfanonin da abin ya shafa za su cimma manufar da ta dace da dokoki, da ka’idojin Sin, da kuma daidaita muradun dukkanin bangarori.
Ta bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum na ma’aikatar kasuwancin a yau Alhamis, yayin da take amsa tambaya game da shirin TikTok na kafa kamfanin hadin gwiwa tare da masu zuba jari na Amurka.
Madam He ta kara da cewa, rukunonin ’yan kasuwar bangarorin biyu, sun riga sun cimma matsaya daya kan yadda za a warware matsaloli kamar batun na TikTok ta hanyar hadin gwiwa. Ana fatan Amurka za ta cika alkawarin da ta dauka, ta samar da yanayi mai kyau na kasuwanci ga kamfanonin Sin dake Amurka, don ba su damar ci gaba da gudanar da harkoki, da kuma inganta ci gaban dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link