Mutum Biyu Sun Mutu Yayin Da Tankar Mai Ta Kama Da Wuta A Titin Legas
[ad_1]
Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar mai (dizal) da safiyar Alhamis a kan Babban titin Badagry, Legas, kamar yadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta tabbatar.
Lamarin ya faru ne a titin Oto-Ijanikin kusa da Jami’ar Ilimi ta Jihar Legas, yayin da wata babbar mota dauke da dizal ta ƙwace yayin da take kokarin wuce wata mota, lamarin da ya sa ta faɗi kuma take ta kama da wuta.
- Manyan Ƙalubale 5 Da Janar Christopher Musa Dole Ya Fuskanta Don Yin Nasara
- Harin Borno: Tabbas Ƴan Ta’adda Za Su Fuskanci Hukunci — Shettima
“Direban Motar da wata mata da ke ciki, duk sun mutu bayan faɗuwar motar.”
Daraktan Wayar da Kan Jama’a na LASTMA, Mista Adebayo Taofiq, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin X na hukumar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce, “Binciken farko ya nuna cewa, lamarin ya faru ne sakamakon gudu mara lissafi, inda aka rahoto cewa, motar ta ƙwace wa direban yayin da yake ƙoƙarin wuce wata mota da ke gabanshi.
[ad_2]
Source link