PDP Ta Maka INEC A Kotu Kan Ƙin Amincewa Da Shugabancin Turaki

[ad_1]

Jam’iyyar PDP, ta bayyana cewa babu wani ɓangare a cikin jam’iyyarta.

Sakataren Yaɗa Labarai na PDP na Ƙasa, Ini Ememobong, ya bayyana haka yayin da yake mayar da martani ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da kin amincewa da Kwamitin Aiki na Ƙasa (NWC) wanda Kabiru Turaki ke jagoranta.

  • Jami’ai Biyu Sun Mutu A Ƙunar Baƙin Wake A Moscow
  • AFCON 2026: Nijeriya Ta Fara Da Ƙafar Dama

INEC ta ce ba za ta amince da zaɓaɓɓun shugabanni jam’iyyar na ƙasa da aka zaɓa a taron ƙasa da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025, a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo ba.

A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 22 ga Disamba, 2025, wacce Sakatariyarta, Dr Rose Oriaran-Anthony ta sanya wa hannu, INEC ta ce ba za ta iya wallafa jerin sunayen shugabannin jam’iyyar PDP da aka zaɓa a shafinta na yanar gizo ba saboda dambarwar jam’iyyar da ke gaban kotu.

Da yake mayar da martani, Ememobong ya ce PDP ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da INEC ta ɗauka na ƙin amincewa da NWC da Turaki ke jagoranta.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *