Rokar Long March-12A Ta Sin Ta Kai Ga Da’irar Da Aka Tsara Bayan Harba Ta Samaniya A Karon Farko
Da safiyar yau Talata ne kasar Sin ta yi nasarar harba rokar Long March-12A zuwa samaniya a karon farko, inda rokar ta shiga da’irar kewayenta kamar yadda aka tsara. Rahotanni sun ce bangare na biyu na rokar ya shiga da’irarsa lami lafiya, ko da yake ba a cimma nasarar gwajin dawo da bangaren farko na rokar ba.
Rokar kirar kasar Sin irinta ta biyu dake aiki da makamashin narkakkiyar iskar oxygen-methane, wadda za a iya amfani da ita wajen dakon kayayyaki, kuma aka yi gwajin dawo da ita doron kasa bayan harba ta a karon farko, ta samar da bayanai masu matukar amfani, da dabaru na zahiri da za su taimaka, wajen inganta maimacin gwaje-gwajen fasaha da za a gudanar da ita a nan gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)